Akalla mutane 30 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka tsere daga gidajensu, sakamakon sabbin hare-hare da aka kai kauyukan Munga da Magami da ke karamar hukumar Karim-Lamido a jihar Taraba.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne suka kai farmakin da sanyin safiyar Asabar, inda suka kone gidaje da lalata dukiyoyi, lamarin da ya kara tayar da hankula musamman bayan kammala babban taron zuba jari da aka gudanar a jihar.
Sai dai maimakon kwanciyar hankali da ci gaba, yanzu haka matsalolin tsaro na kara fantsama a fadin jihar, lamarin da ke jefa sabanin ra’ayi kan yadda gwamnati ke tunkarar rikice-rikicen da ke faruwa.
Wasu daga cikin wadanda suka tsira da ransu sun bayyana takaicinsu kan yadda gwamnatin jihar ke tafiyar da lamuran tsaro, inda suka nuna rashin jin dadinsu da rashin zuwan Gwamna Agbu Kefas yankin da lamarin ya faru, suna kuma kwatanta shi da Gwamnan Borno, Babagana Zulum, wanda aka fi sanin sa da kai ziyara wuraren rikici kai tsaye.
A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan yada labarai da fasahar sadarwa, Emmanuel Bello, ya fitar, Gwamna Kefas ya bayyana harin da cewa “mugun abu ne kuma ba za a amince da shi ba.” Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta dauki mataki na gaggawa don gurfanar da wadanda suka aikata laifin.
Sabbin Hare-Hare a Taraba Sun Yi Ajalin Mutane Fiye da 30
