An kama wani mutum ɗauke da bindiga a cikin wata coci a jihar Filato

Jami’an hukumar tsaro ta NSCDC wato Civil Defense sun kama wani mutum dake ɗauke da bindiga a wata Church dake ƙaramar hukumar Bokkos ta jihar Filato a ranar Lahadi.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 08:30 na safe lokacin da jami’an bisa dogaro da bayanan sirri da suka samu nasarar kama lokacin da suke gudanar da sintirin da suka saba a kusa da harabar cocin.

“An kama wanda ake zargin ɗauke da bindiga kuma ya gaza yin gamsasshen bayani ko kuma  nuna wata sheda a hukumance da ta amince masa ɗaukar bindigar,” a cewar wani jami’in Civil Defense.

Lamarin na zuwa ne dai-dai lokacin da jihar ke cigaba da fuskantar karin yawan hare-hare da suka haifar da asarar rayuka masu yawan gaske.

More from this stream

Recomended