‘Yan Ta’adda Sun Lalata Gadar Mandafuma a Maiduguri

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne masu alaka da ISWAP sun tarwatsa Gadar Mandafuma da ke kan hanyar Biu zuwa Damboa a jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, inda aka dasa bam ɗin IED a gadar, wanda hakan ya kai ga rushewar ta baki daya.

Zagazola Makama, wani kwararre a fannin yaki da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, ya bayyana hakan a cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba.

Ya ce, “Wannan aikin ta’addanci an yi shi ne da nufin dakile zirga-zirgar ababen hawa da fasinjoji a hanyar, tare da hana samun saukin shiga yankin.”

Makama ya kara da cewa harin na da nufin hana karfin gwiwar sojojin da ke kokarin kai dauki ta hanyar, yana mai cewa “lamarin yana shafar shirin soji na karfafa tsaro a yankin.”

Wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da yankin Arewa maso Gabas ke fuskantar kalubale daga hare-haren kungiyoyin ta’addanci, musamman a jihar Borno.

More from this stream

Recomended