Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta dakile wani harin da ‘yan bindiga suka kai garin Keta da ke Karamar Hukumar Tsafe, inda ta kashe adadi mai yawa daga cikinsu, ciki har da shahararren shugaban ‘yan bindiga, Dan Mudale.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Yazid Abubakar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau, babban birnin jihar.
Ya ce da misalin karfe 3:40 na yamma, wani mutum mai kyakkyawar niyya ya sanar da ‘yan sanda cewa gungun ‘yan bindiga dauke da makamai sun afka garin Keta da nufin aikata ta’addanci.
“Da samun wannan bayani, rundunar hadin gwiwa da ke dauke da jami’an Mobile Police, sashen Counter Terrorism, farauta da kuma masu tsaron al’umma sun garzaya suka fafata da ‘yan bindigar a musayar wuta mai tsanani,” in ji DSP Abubakar.
A yayin artabun, wani dan sanda guda daya, tare da membobi hudu na kungiyar tsaron al’umma da kuma wasu mafarauta biyu, sun rasa rayukansu. Sai dai kuma wasu mafarauta biyu na karbar kulawa a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gusau.
Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar wa jama’a da cewa tana kokarin ganin an dawo da zaman lafiya a jihar, tare da yin kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da hadin kai ta hanyar sanar da hukumomi duk wani motsi da ba su yarda da shi ba.
‘Yan Sanda Sun Kashe Fitaccen Shugaban ‘Yan Bindiga, Dan Mudale, a Zamfara
