Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutun Ƙaramar Sallah

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun Litinin da Talata a matsayin ranakun hutun shagulgulan bikin Karamar Sallah.

Magdalene Ajani babbar sakatariyar dindindin a ma’aikatar harkokin cikin gida ita ta sanar da ranakun hutun a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.

Sanarwar da ta fitar ta ce ministan harkokin cikin gida Olabunmi Tunji ya shawarci Musulmai da su rungumin dabi’un jinkai, yin alkhairi da kuma zaman lafiya..

Har ila yau ministan ya shawarci ƴan Najeriya da su yiwa ƙasa addu’ar zaman lafiya da yalwar arziki a lokacin bikin sallar ya ƙara da cewa yakamata bikin sallar ya samar da hadin kai da kuma aiki tare da juna.

More from this stream

Recomended