Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, ta shirya gurfanar da mutum 37 da ake zargi da aikata zamba ta intanet a Jihar Kwara.
Wadanda ake zargin an kama su ne a wani samame da EFCC ta kai a wurare daban-daban a jihar, bayan samun rahotanni da suka nuna yadda suke damfarar mutane ta hanyar intanet.
A cewar jami’an hukumar, an samu wasu daga cikin su da katunan ATM, wayoyi, kwamfutoci, da kuma wasu takardu da ake zargin suna amfani da su wajen aikata zamba.
Hukumar ta bayyana cewa za a gurfanar da su a gaban kotu nan ba da jimawa ba, bisa laifuka da suka shafi damfara, amfani da bayanan karya, da kuma karɓar kuɗi ta haramtacciyar hanya.
Hukumar EFCC Za Ta Gurfanar da Mutum 37 Bisa Zargin Zamba ta Intanet a Jihar Kwara
