Ƴan fashin daji sun kashe mutane 12 a Zamfara

Jami’ai 12 na hukumar tsaro ta jihar Zamfara da kuma ƴan bijilante aka rawaito an kashe a wata arangama da suka yi da ƴan fashin daji a ƙauyen Adabka dake ƙaramar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun bayyana cewa wasu da dama kuma sun samu raunin harbin bindiga kuma an garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci.

A yayin da suma ƴan fashin dajin aka yi musu ɓarna sosai mazauna yankin sun ce baza su iya sanin yawan mutanen da aka kashe musu ba saboda sun tafi da gawarwakin da kuma waɗanda suka jikkata.

Mallam Fahad wani mazaunin ƙauyen Sabuwar Tunga ya ce tun da farko ƴan fashin dajin sun kai farmaki garinsu da wajen ƙarfe 09:00 na safiyar ranar Laraba inda suka yi awon gaba da mutane da dama ciki har da mata.

Ya ce a lokacin da suke ƙoƙarin tafiya ne su kayi arba da jami’an tsaro inda suka ɗauki tsawon watanni suna ɗauke ba daɗi har ta kai ga kisan ƴan bijilante tare da samun nasarar ceto wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwar da su.

More from this stream

Recomended