
Ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu ɗalibai mata na jami’ar Joseph Sarwuan Tarka dake Makurdi babban birnin jihar Benue.
Ɗaliban da yawansu ya kai huɗu anyi garkuwa da su da maraicen ranar Talata a ginin jami’ar na North Core Campus.
Wata majiya ta ce ɗaliban sun tafi aji ne domin yin karatun dare lokacin da aka yi garkuwar da su.
Ƴan bindigar sun farma bangaren otal na jami’ar kafin su yi awon gaba da ɗaliban.
Mintoci kaɗan bayan faruwar dakarun rundunar sojan Najeriya sun isa makarantar.
Sewuese Aneneh mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ta faɗawa jaridar The Cable cewa labarin da ya same su ya nuna cewa dalibai biyu ne kawai aka yi garkuwa da su.
Aneneh ta ƙara da cewa tuni rundunar ƴan sanda ta kaddamar da bincike kan faruwar lamarin.