Dalibi 1 ya mutu 4 sun jikkata a fashewar wani abu a wata makarantar islamiyya a Abuja

Fashewar wani abu a wata makaranta dake Abuja ya jawo mutuwar dalibi ɗaya tare da jikkata wasu huɗu.

Wata majiyar jami’an tsaro ta bayyana cewa fashewar abun ta faru da misalin ƙarfe 12:00 na rana a wata makarantar Islamiyya dake garin Kuchibiyu a ƙaramar hukumar Bwari.

Jami’an ƴan sanda kwance bam da kuma na bada agajin gaggawa sun gaggauta zuwa wajen da lamarin ya faru.

An garzaya da waɗanda suka jikkata ya zuwa asibiti har ya zuwa lokacin wallafa wannan labarin rundunar ƴan sandan birnin bata fitar da wata sanarwa ba kan faruwar lamarin.

Duk ƙoƙarin jin ta bakin hukumomin makarantar ya ci tura.

More from this stream

Recomended