
Rundunar ƴan sandan jihar Benue ta kama wasu mutane biyu da ake zarginsu da hannu a kisan wata tsohuwar mata wacce ake zargi mayya ce a ƙauyen Egba dake ƙaramar hukumar Agatu ta jihar.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Catherine Anene ta tabbatar da kama wani mai suna Bako mai shekaru 50 da kuma Oyaje Clement mai shekaru 40 kan hannu da su ke da shi a kisan kan.
Anene ta bayyana kisan a matsayin wani yayi da ake mai tayar da hankali na ɗaukar doka a hannu musamman kan tsofaffi da ake zargi da aikata maita.
“Ƙarin wata damuwa mai tayar da hankali a jihar shi ne yadda mutane su ke ɗaukar doka a hannunsu musamman matasa dake kashe dattawa bisa zargin maita,” ta ce.
“A ranar 24 ga watan Disamba 2024 da misalin ƙarfe 07:00 na dare mun samu labarin kisan wata dattijuwa kan zargin maita a ƙauyen Egba dake ƙaramar hukumar Agatu biyo bayan bincike an kama mutane biyu da ake zargi da hannu akan kisan,”.