Kotu ta bayar da belin Yahaya Bello

Wata babbar kotun tarayya dake Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello kan kudi miliyan ₦500

An gurfanar da Bello ne a gaban kotun inda ake masa to tuhumar al-mundahanar kuɗaɗen da yawansu ya kai sama naira biliyan 110.

Da take yanke hukunci kan buƙatar Bello ta neman belin alkaliyar dake sauraren ƙarar, mai shari’a, Maryam Anenih ta ce dole kuma tsohon gwamnan ya kawo mutane biyu ƴan Najeriya nagartattu da za su tsaya masa.

Har illa yau dole ne mutanen su zama suna da gida ko kadara a cikin ɗaya daga cikin unguwannin Guzape, Wuse 2, Apo, Asokoro da kuma Jabi dake birnin tarayya Abuja.

Har ila yau za su miƙa hotunan fasfo biyu da kuma shedar katin dan kasa.

More from this stream

Recomended