Ƴan sanda sun kashe mutane 4 tare da kama 5 a maɓoyar masu garkuwa da mutane

Rundunar ƴan sandan jihar Imo ta ce ta kashe wasu mutane huɗu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ƙauyen Ezioha dake garin Eziama a ƙaramar hukumar Mbaitoli ta jihar.

A wata sanarwa ranar Litinin, Henry Okoye mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya ce jami’an ƴan sandan sun kama wasu mutane da ake zargin su da aikata laifi inda aka same su da bama-bamai, baburan hawa 8 na’urorin sadarwa a wani dame da aka kai a ranar Talata.

Okoye ya ce an samu gagarumar nasarar ne a samamen na haɗin gwiwar jami’an hukumar NSCDC, DSS da kuma ƴan sanda a ƙarƙashin rundunar tsaro ta Operation UDO KA.

Aboki Danjuma, kwamishinan ƴan sandan jihar ya jaddada aniyar rundunar na kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar.

More from this stream

Recomended