Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta ce jami’anta sun samu nasarar kama wasu mutane biyu a cikin Maiduguri kan titin Damboa da ake zargin su da sace wayoyin hannu 25.
A wata sanarwa ranar Laraba mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, Nahum Daso ya ce an kama mutanen ne a wurin wani shingen binciken ababen hawa.
Daso ya ce jami’an kar ta kwana na rundunar sune su ka kama mutanen a cikin wani Babur mai ƙafa uku a ranar Talata.
Mai magana da yawun rundunar ya ce jami’an sun gano wayoyi iri daban-daban a yayin binciken ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifin ƙwace wayoyin mutane a jihohin Adamawa da Borno.
Wasu daga cikin garuruwan da mutanen su ke ƙwacen wayar sun haɗa da Mubi, Tashan Alade, Miringa, Kwaya Kusar da kuma ƙaramar hukumar Biu ta jihar.
“Rundunar Ƴan Sandan ta fara ƙoƙarin miƙa wayoyin da aka gano ga mallaka su,” a cewar sanarwar.