Jirgin saman Max Air ya yi saukar gaggawa a Maiduguri

Wani jirgin saman kamfanin Max Air ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Maiduguri jim kaɗan bayan tashin sa daga filin jirgin saman Muhammad Buhari dake birnin.

A cewar wasu bayanai lamarin ya faru ne da maraicen ranar Alhamis lokacin da jirgin ya ɗauki fasinjoji daga filin jirgin saman akan hanyarsu ta zuwa Abuja amma sai injinsa ya kama da wuta abin da ya tilastawa matukan jirgin dawowa su yi saukar gaggawa.

Fasinjoji 80 ne a cikin jirgin a cikinsu akwai matakin gwamnan jihar Borno, Ahmad Kadafur.

Babu wani daga cikin fasinjojin da ya jikkata a lamarin.

Mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Dogo Shettima ya tabbatar da cewa mai gidansa yana cikin ƙoshin lafiya.

Ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin saman, Lucy Dlama wacce ke rike da mukamin mai bawa gwamnan jihar Borno shawara kan harkokin mata ta tabbatar da faruwar lamarin.

“Muna cikin tafiya kawai sai muka ji wata ƙara sai kuma jirgin ya fara tangal-tangal  lokacin da muka fara ganin tartsatsin wuta,”

More from this stream

Recomended