Ƴan sanda a jihar Zamfara sun samu nasarar kama wani ɗan ƙasar Algeriya dake safarar makamai a tsakanin ƙasa da ƙasa.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Muhammad Dalijan shi ne ya bayyana haka ranar Talata a Gusau babban birnin jihar.
Ya ce ƴan sanda sun samu nasarar ƙwace bindigogi ƙirar AK-47 guda 16 a farmaki daban-daban da su ka kai a jihar a cikin makonni uku da su ka wuce.
Ya ƙara da cewa rundunar ta gano bindiga ƙirar dobul barel da kuma ƙaramar fistol ƙirar gida daga wurin wani mai ƙera bindigogi dake garin Jos a jihar Filato.
“Rundunar bisa dogaro da bayanan sirri ta bi diddigi ta gano tare da kama mai ƙera makamai a garin Jos ta kuma bi diddigi tare da kama mai safarar makamai ɗan ƙasar Aljeriya akan iyakar garin Illela,” ya ce.
“Ɗan Aljeriyan da aka kama ya faɗawa ƴan sanda cewa ya shafe shekaru takwas yana aikata wannan sana’a.”
“Yana samar da makami da harsashi ga dukkanin ƴan fashin dajin da suke yankin arewa maso yamma a lokacin da aka kama shi bindiga ƙirar AK-47 guda huɗu aka samu tare da shi,” a cewar kwamshinan.
Har ila yau rundunar ƴan sandan ta ce ta kama wasu mutane dake aikin haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.