Rundunar sojan Ruwan Najeriya ta karɓi wasu jirage uku masu saukar ungulu ƙirar Agusta Westland(AW) 109 Trekker daga ma’aikatar tsaron Najeriya.
Aiwuyor Adams-Aliu daraktan yaɗa labarai na rundunar sojan ruwa a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce an miƙa jiragen ne a ranar Talata a wurin ajiye jirage na kamfanin Caverton dake Ikeja a jihar Lagos.
Aliu ya ce jiragen an ƙera su dauke da dukkanin abun da ake buƙata na manyan ɓakin alfarma da suka haɗa da kujerun fata masu laushi da kuma kayayyakin hana jin ƙugin jirgin..
Ya ƙara da cewa jiragen suna da ƙarin wani tankin mai da zai basu damar tafiya ta tsawon sa’o’i 3 da minti 45.