9.7 C
London
Thursday, November 7, 2024
HomeHausaRundunar ƴan sandan Najeriya ta samu gagarumar nasara a yaƙi da masu...

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta samu gagarumar nasara a yaƙi da masu aikata laifi

Date:

Related stories

Babban lauya Femi Falana zai nemi a biya diya ga yaran da aka sako

Babban lauya maikare hakkin bil'adama, Femi Falana  ya ayyana...

Buhari ya kai ziyarar jajen ambaliyar ruwa jihar Borno 

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya kai ziyarar jaje...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Shettima ya gana da yaran da  aka sako a fadar Aso Rock

Yaran da aka gurfanar a gaban kotun kan zanga-zangar...

Tinubu ya bada umarnin sakin yaran da aka gurfanar a gaban kotu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin ...
spot_imgspot_img

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce ta kama, Jubril  Musa wani babban mai dillancin bindigogi a jihar Filato.

A wata sanarwa ranar Alhamis, Olumiyiwa Adejobi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya, ya ce an kama Musa ne ɗauke da tarin makamai.

Ya ƙara da cewa wanda aka kama ɗin ya amsa cewa yana samar da makamai ga ƴan fashin daji da kuma masu garkuwa da mutane.

Adejobi ya ƙara da cewa cikin wata guda ƴan sanda sun kama mutane da dama dake da hannu a aikata laifukan da suka haɗa da fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma kisan kai.

“Tun daga 1 ga watan Oktoba 2024 Rundunar Ƴan sandan Najeriya ta samu gagarumar nasara a yaƙin da take da aikata laifukan,” ya ce.

“Waɗannan sun haɗa da mutane 371 da ake zargi da aikata fashi da makami, mutane 186 masu garkuwa da mutane, mutane 242 da ake zargi da kisan kai, mutane 63 da suka mallaki bindiga ba tare da ka’ida ba da kuma mutane 217 da ake zargi da aikata fyade.”

Ya cigaba da cewa rundunar ta kuma samu nasarar gano motocin sata 118 da kuma kuɓutar da mutane 64 da aka yi garkuwa da su a faɗin ƙasarnan.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories