Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana damuwarsa kan matsalar rashin wutar lantarki da ake fama da ita a yankin arewacin Najeriya.
Shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan kafafen yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar.
Sanarwar ta ce shugaban ƙasar ya ɗauki gaɓarar shigewa gaba wajen ƙoƙarin yin duk mai yiyuwa domin gyaran wutar lantarkin da rashin ta ya jefa miliyoyin mutane a cikin wani mawuyacin hali.
Tuni shugaban ƙasar ya gayyaci ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu da kuma mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu inda ya tattauna da su kan yadda za a shawo kan matsalar.
Shugaban ƙasar ya umarci ministan da su hanzarta aikin da suke yi na gyaran wutar domin ganin an dawo da wuta a yankin na arewacin Najeriya.
Domin ta tabbatar da cewa aikin yana tafiya ba tare da tsaiko ba, Shugaba Tinubu ya umarci mai bashi shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da ya haɗa kai da rundunar sojan saman Najeriya da kuma rundunar soja domin bayar da cikakken tsaro ta ƙasa da ta sama ga injiniyoyin da za su gudanar da aikin gyaran.