An sako tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru biyar da kotu ta yanke masa kan zargin aikata cin hanci da rashawa.
Lawan wanda ya kasance shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai ta tarayya da aka naɗa domin ya binciki badaƙalar kuɗin tallafin man fetur a shekarar 2012 an yanke masa ɗaurin zaman gidan yari bayan da ya karbi toshiyar baki ta $500,000 daga fitaccen ɗan kasuwan nan Femi Otedola domin ya wanke kamfaninsa na Zenith Oil daga dukkanin zarge-zargen da ake wa kamfanin.
An kuma tura shi gidan yari a shekarar 2021 bayan da aka same shi laifin neman a bashi toshiyar baki har dalar Amurka miliyan $3 daga hannun Otedola.
Fefan bidiyon da Otedola ya saki a matsayin sheda ya nuna yadda Lawan yake cusa kuɗin da aka bashi a cikin babbar rigarsa da kuma ƙasan hula.
Bayan sakin nasa Lawan ya miƙa godiyarsa ga Allah da yan uwa da kuma abokan arziki bisa yadda suka kasance da shi a cikin halin da ya samu kansa.
Ya ce a yanzu ya bude wani sabon shafi na rayuwarsa bayan fitowarsa daga gidan yarin.