Sanata Abdulrahaman Kawu Sumaila dake wakiltar mazaɓar Kano ta kudu a majalisar dattawa ya ce a duk wata ana biyansa naira miliyan 21 a matsayin albashi da wasu kuɗaɗen gudanar da ayyukan yau da kullum.
A wata tattaunawa da yayi a gidan rediyon BBC Hausa ya bayyana cewa albashinsa a hukumance bai wuce naira miliyan ɗaya ba kamar yadda hukumar RMAFC dake tattarawa da rabon arzikin ƙasa ta kayyade kuma hakan na komawa kusan N600,000 idan aka cire haraji da sauransu amma kuma akwai wasu alawus da suke sakawa kuɗin da ake basu ya kai naira miliyan 21 duk wata.
Hakan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan da hukuma ta RMAFC da doka ta bata damar kayyade albashin duk wani mai riƙe da muƙamin siyasa ta yi iƙirarin cewa ana biyan kowane sanata daga cikin sanatoci 109 naira miliyan ɗaya da dubu sittin a duk wata a matsayin albashi.
Ɗan majalisar ya ce alawus ɗin da ake biyansu ya haɗa kuɗin jarida, kuɗin gudanar da ofishinsu na tafiye-tafiye a sauransu.
Hakan na zuwa ne biyo bayan kalaman da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi inda ya ce ba dai-dai bane ƴan majalisar ƙasa su riƙa sakawa kansu albashin da suka ga dama.