Ƴansanda sun tabbatar sojoji sun kashe wani matashi a Bauchi

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da kisan wani mai suna, Aminu Habibu da dakarun sojan rundunar samar da tsaro ta Operation Safe Haven suka yi a yayin wata arangama da wasu matasa a garin Lere dake ƙaramar hukumar Tafawa Balewa ta jihar.

Wani shedar gani da ido ya faɗawa jaridar Daily Trust cewa an kashe mutum ɗaya a yayin da wasu 6 suka jikkata sakamakon harbin bindiga lokacin da sojoji suka kai samame gidan wasu matasa da ake zargin su da shiga faɗan da ya faru a shingen binciken ababen hawa dake hanyar shiga garin.

Mai magana da yawun rundunar SP Ahmad Wakili ya faɗawa jaridar Daily Trust cewa ana gudanar da bincike kan lamarin.

Rikicin ya samo asali ne sakamakon sabani da aka samu da wasu ƴaƴan jam’iyar PDP daga ƙauyen na Lere da kuma jami’an na Operation Safe Haven da aka a jiye a Tafawa Ɓalewa.

Wakili ya ce rundunar za ta gudanar da bincike domin gano jami’in sojan da ya aikata kisan.

More from this stream

Recomended