Mambobin majalisar wakilai ta tarayya sun amince su rage albashinsu da kaso 50 na tsawon watanni 6 a matsayin nasu sadaukarwar da kuma nuna goyon baya kan halin matsin tattalin arziki da ƴan Najeriya suke fuskanta.
Sun dauki matakin ne biyo bayan gyara kan buƙatar kuɗirin da mataimakin shugaban majalisar Benjamin Kalu ya gabatar kan buƙatar ƴan majalisar su sadaukar da kaso 50 rabin albashi na ₦600,000 domin tallafawa ƴan Najeriya duba da halin matsin da ake ciki.
Kalu ya yi gyara kan ƙudirin ne biyo bayan kuɗirin da wakili Isiaka Ayokunle da ya yi kira kan masu kiran yin zanga-zanga da su jingine batun su tattauna da gwamnati.
Hakan na nufi albashin yan majalisar zai ragu da naira miliyan ₦108 a kowane wata.