Tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman ya yanke jiki ya faɗi a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja.
Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta’annati ce ta gurfanar da shi a gaban kotu inda take masa tuhume-tuhume 12 da suka shafi al-mundahanar kuɗaɗe da yawansu ya kai biliyan 33,804,830,503.
Gabanin fara sauraren shari’ar,Femi Ate lauyan Mamman ya faɗawa alƙalin kotun James Omotosho cewa wanda yake karewa ya yanke jiki ya faɗi saboda rashin lafiya.
A yayin da aka cigaba da zaman shari’ar tsohon ministan ya shiga kotun kayansa a jiƙe inda ya wuce cikin akwatun da mutanen da ake tuhuma suke tsayawa.
Alƙalin kotun ya tambayi Mamman da dalilin da yasa yake gumi ko kuma anyi ruwa ne.
Tsohon ministan ya ce ruwa aka zuba masa.