Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya dakatar da Hon. idrissa Mai Bukar shugaban karamar hukumar Machina makonni 3 bayan da aka rantsar da shi tare da sauran ciyamomin da aka zaba a zaɓen ƙananan hukumomin jihar na ranar 09 ga watan Yuni.
Sakataren yaɗa labaran sakataren gwamnatin jihar, Shu’aibu Abdullahi shi ne ya sanar da dakatarwar cikin wata sanarwa da ya fitar..
Abdullahi ya ce gwamna Buni ya yi amfani da ƙarfin ikon da sashe 2 na dokar ƙananan hukumomi ta shekarar 2019 da aka yiwa gyara ya bashi wajen dakatar da Bukar saboda nuna rashin ɗa’a da kuma ƙin yin biyayya.
Gwamna Buni ya umarci dakataccen shugaban ƙaramar hukumar da ya miƙa ragama mulki ga mataimakinsa kana ya jiraci umarni na gaba.