An sake zaɓen Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS

An sake zaɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaban ƙungiyar tattalin arzikin ƙasashen  Afrika ta yamma wato ECOWAS.

An zaɓi Tinubu a matsayin sabon shugaban ƙungiyar a wurin taron shugabannin kasashen karo 65 da aka gudanar a fadar Aso Rock dake Abuja.

A cikin watan Yulin shekarar 2023 aka fara zaɓen Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS a wani taron da aka gudanar a ƙasar Guinea-Bissau.

Tinubu shi ne shugaban Najeriya na 8 dake jagorantar ƙungiyar ta ECOWAS.

Sake zaɓen Tinubu na zuwa ne dai-dai lokacin da ƙungiyar ke fuskantar ƙalubalen juyin mulki a wasu ƙasashe mambobin ƙungiyar.

More from this stream

Recomended