Biyo bayan shafe sa’o’i da dama ana ganawa ranar Juma’a gwamnatin tarayya da kuma ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu sun ƙara tayin da suka yi na mafi ƙarancin albashi daga ₦60,000 zuwa ₦62,000.
Amma kuma gamayyar kungiyoyin ƙwadago sun miƙa tayin ₦250,000 ragi daga ₦494,000 da suka bukaci a riƙa biya a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Hakan ne ya kawo ƙarshen taron ganawar da kwamitin ɓangarori da uku da gwamnatin tarayya ta kafa bayan watanni da dama.
Za miƙa matsayar da aka cimma ga shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu wanda ake sa ran zai tura kuɗirin dokar sabon ƙarin albashin ga majalisar ƙasa.
A wani ɓangaren gwamnonin Najeriya ƙarƙashin ƙungiyar su sun fitar da wata sanarwa dake cewa baza su iya ₦60,000 ba a matsayin mafi ƙarancin albashi.