Tinubu Ya Dawo Abuja Daga Ziyarar Aiki Da Ya Kai  Saudiya da Nezaland

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya dawo Abuja bayan ziyarar aiki da ya kai ƙasashen Saudiya da Nezaland.

A ranar 22 ga watan Afrilu ne shugaban ƙasar ya bar birnin tarayya Abuja ya zuwa ƙasar Nezaland inda ya kai ziyarar aiki.

A lokacin mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya ce Tinubu ya kai ziyarar ne biyo bayan gayyatar da firaministan ƙasar , Mark Rutte ya yi masa.

Bayan kammala ziyarar ta Nezaland shugaban ƙasar ya wuce ƙasar Saudiya inda ya halarci taron tattalin arziki duniya da aka gudanar a ranakun 28 da 29 ga watan Afrilu.

Tun bayan halartar taron ne ba a ƙara jin ɗuriyar shugaban kasar ba inda wata majiya dake kusa da shugaban ta bayyana cewa ya wuce birnin Paris na ƙasar Faransa a wata ziyara ta ƙashin kansa.

Hakan  ya sa wasu ƴan adawa ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar suka fara kiraye-kirayen da a bayyana inda shugaban ƙasar ya ke.

More from this stream

Recomended