Dakarun sojan Najeriya dake aiki da rundunar samar da tsaro ta Operation Desert Sanity III sun samu nasarar ceto, Lydia Simon ɗaya daga cikin ƴan matan Chibok da mayaƙan Boko Haram suka sace a shekarar 2014.
Rahotanni sun bayyana cewa an ceto Lydia ne tare da ƴaƴanta guda uku a ƙaramar hukumar Ngoza ta jihar Borno.
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro an yankin tafkin Chadi, Lydia na daga cikin matan da suka tsere daga sansanin ɗan ta’addar nan Ali Ngulde dake tsaunukan Mandara inda ake tsare da ita na tsawon shekaru.
Ta miƙa kanta ga dakarun sojan bataliya ta 82 dake Ngoshe a ƙaramar hukumar Gwoza yarinyar da aka ceto tana ɗauke da ciki ɗan wata biyar kuma tayi iƙirarin cewa ta fito ne daga garin Pemi dake Chibok.