Sojojin Najeriya sun kashe ƴanta’adda a Arewa maso Yamma

Dakarun sojojin Najeriya a wani samame daban-daban da suka kai a jihohin Zamfara da Katsina sun kashe ‘yan ta’adda 11.

A garin Zamafara, an kai samame maboyar wani shugaban ‘yan ta’adda, Hassan Yantagwaye, a karamar hukumar Tsafe, wanda ya yi sanadin fafatawa da ‘yan ta’addan guda biyu a harin.

Hakan na kunshe ne a wani sako da rundunar sojin Najeriya ta fitar a ranar Litinin.

A cewar saƙon, “Dakarun Sojojin Najeriya da aka tura domin Yaki da Ta’addanci a Jihohin Katsina da Zamfara, a wani jerin hare-hare na hadin gwiwa sun kai farmaki a yankunan ‘yan ta’adda wanda ya yi sanadin kawar da dimbin ‘yan ta’adda.

“A wani samame da suka kai jihar Zamfara, a ranar 29 ga Maris, 2024, sojoji sun yi nasarar kai samame a kogon wani fitaccen sarkin ‘yan ta’adda, Hassan Yantagwaye, a karamar hukumar Tsafe.

“A yayin farmakin, sojoji sun fatattaki ‘yan ta’addan a wani artabu da suka yi da su, inda suka kashe uku daga cikinsu tare da kwato tarin makamai da alburusai.  Sojojin sun kuma lalata sansanonin ‘yan ta’addan.”

More from this stream

Recomended