Gwamnan jihar Kano,Engr Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da shirin raba fom ɗin jarrabawar UTME ga ɗaliban sakandaren jihar dubu 6500.
A wata sanarwa gwamnan ya ce ya yi hakan ne domin samar da damarmaki ga ɗaliban jihar na halartar makarantun da suke gaba da sakandare.
“A ƙoƙarin mu na samar da damarmaki na cigaba da karatun gaba da sakandare ga ƴan asalin jihar Kano na ƙaddamar da rabon fom ɗin jarrabawar JAMB UTME guda 6500 ga ɗaliban makarantun sakandare,” ya ce.
Ya ce gwamnatinsa ta samu cimma manyan nasarori a bangaren bunƙasa ilimi a jihar a cikin watanni goman da suka gabata da suka haɗa da dawo da shirin tura ƴan asalin jihar ƙaro karatu a jami’o’in ƙasashen waje, biyan kuɗin makaranta na ɗaliban jihar dake manyan makarantu da sake buɗe makarantu 21 na koyon sana’a.