Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta kama wani mai suna, Rabi’u Adamu da ake zargi da yin garkuwa da kuma kisan wani yaro ɗan shekara 12 ɗan gidan ASP Bala Yarima.
A wata sanarwa ranar Juma’a, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar,Ahmed Wakili ya ce wanda ake zargi mai shekaru 21 ya yi garkuwa tare da kashe Christopher Musa dake garin Magaman Gumau.
Wakili ya ce anyi garkuwa da marigayin ranar ranar 21 ga watan Maris lokacin da aka aike shi.
” A ranar 21 ga watan Maris 2024 da ƙarfe 08:00 na safe rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta samu kiran kai ɗaukin gaggawa na yin garkuwa da Christopher Bala ɗan gidan ASP Bala Yarima a garin Gumau,” a cewar sanarwar.
Biyo bayan binciken farko da aka yi wanda ake zargin ya amsa laifin shaƙe wuyan Christopher har ya mutu kuma ya amsa laifin tatsar kuɗi har naira 200,000 daga mahaifin yaron.
Wanda ake zargin ya ce bayan da ya fuskanci cewa marigayin ya gane shi hakan ne ya sa ya kashe shi inda ya binne shi kusa da wani tsauni dake ƙauyen Bazale.