Gwamnan jihar Bauchi,Bala Muhammad ya sanar da yiwa maniyatan Aikin Hajji da suka fito daga jihar ragin ₦900,000 kan kuɗi aikin da za su biya.
Muhammad ya sanar da haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.
Sanarwa ta ce an ɗauki matakin ne la’akari da kuncin rayuwa da kuma matsi da ake fama da shi.
Kuɗin da gwamnan ya bawa maniyatan na nufin kaso 50 cikin 100 na ƙarin da Hukumar Aikin Hajji Ta Ƙasa NAHCON ta yi kan kuɗin kowace kujera.
“La’akari da halin kunci da tsadar rayuwa da muka tsinci kan mu a ciki, na sanar da biyan rabin karin kudin da hukumar kula da jin dadin alhazai ta kasa wato NAHCON ta bukaci kowane maniyyaci ya biya.”a cewar sanarwar
“Na biya wa kowane maniyyacin jihar Bauchi tallafın naira dubu dari tara da hamsin, wato kaso 50% na karin kudin, sannan na umurci hukumar a matakin jiha da ta mayar wa kowane maniyyaci kwatan-kwacin tallafın da muka biya, wadanda ba su biya karin ba kuma su cire kafın cikar wa’adin da aka diba.”