MTN yana ƙoƙarin ƙara kuɗin kati da data a Najeriya

Katafaren kamfanin sadarwa na MTN na kokarin kara kudin katin waya da na data a Najeriya.

Kamfanin sadarwa mafi girma a nahiyar Afirka ya ba da rahoton raguwar ribar da ake samu a duk shekara a ranar Litinin, sakamakon hasarar da ya samu bayan harajin da ya kai Naira biliyan 137 da ayyukanta na Najeriya ke yi da kuma karin kudin gudanar da aiki.

Shugaban Kamfanin na MTN, Ralph Mupita, ya ce tuni kamfanin ya fara tattaunawa da hukumomin Najeriya kan hakan.

“Bisa bayanin yadda ake kashe kudaden mu a Najeriya, muna bukatar karin kudin fita don rage farashin tafiyar da hanyoyin sadarwa,” in ji Mupita. 

More from this stream

Recomended