Gwamnan jihar Kano, Engr Abba Kabir Yusuf ya koka kan yadda ake sarrafawa tare da raba abincin ciyarwar watan Azumi a jihar da gwamnatin Kano ta samar.
A yayin wata ziyarar bazata zuwa ɗaya daga cikin cibiyoyin da ake dafawa tare da raba abincin dake ƙaramar hukumar Municipal gwamnan ya nuna rashin gamsuwarsa kan irin abinci da ake dafawa ake bawa jama’a.
Ya yi zargin ana zagon ƙasa a shirin inda ya ɗora ayar tambaya kan yawa a da kuma ingancin abincin da ya gani ba kamar wanda gwamnati ta amince a bayar ba.
Gwamnan ya gargadi masu dafa abinci dama wanda ya basu aikin da kada su kuskura su sake dafa makamancinsa.
Gwamna Yusuf ya umarci shugaban ma’aikatansa Shehu Wada Sagagi da ya sa ido kan yadda shirin ke gudana tare da bashi rahoton cigaban da ake samu a kullum.