Gwamnatin jihar Katsina ta ce mata 10 ne da kuma ƙananan yara tara aka ceto daga cikin mutanen da ƴan fashin daji suka yi garkuwa da su watan da ya wuce.
Gwamnatin ta ce dakarun rundunar sojan Najeriya ne suka samu nasarar ceto mutanen.
A ranar 3 ga watan Faburairu mutane 55 ne aka yi garkuwa da su lokacin da suke kan hanyar raka wata amarya dakinta zuwa garin Damari a ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar.
Ƴan kwanakin da suka wuce wani fefan bidiyo ya karaɗe kafafen soshiyal midiya inda masu garkuwar suka yi barazanar aurar da amarya matukar ba a fanshe ta ba.
A wata sanarwa ranar Litinin, Ibrahim Kaulaha mai magana da yawun gwamnan jihar Katsina,ya ce waɗanda aka ceton an miƙa su ga hannun shugaban ƙaramar hukumar Sabuwa ta jihar.
Mohammed ya ce Dikko Radda ya yabawa sojojin kan bajinta da suka nuna wajen aikin ceto mutanen