Shugaban Jam’iyar APC Na Jihar Ekiti Ya Mutu

Shugaban jam’iyar APC na jihar Ekiti, Paul Omotoso ya mutu .

Wata majiya dake kusa da iyalinsa ta ce Omotoso ya mutu ne da tsakar daren ranar Laraba bayan gajeriyar rashin lafiya.

An bada rahoton cewa ya halarci wani taron siyasa ranar Litinin inda aka garzaya da shi asibiti a Ado-Ekiti a ranar Talata bayan da yayi ƙorafin cewa yana jin zazzaɓi. Ya mutu a asibitin Ado-Ekiti.

A wata sanarwa tsohon gwamnan jihar, Kayode Fayemi ya bayyana Omotoso a matsayin ” Shugaba mai sadaukar da kai, mai hada kan mutane kuma jigon jam’iyar APC a jihar.”

Fayemi ya ce ” Mutuwar shugaban jam’iyar rana tsaka ta bar giɓi da za a wahala  kafin a cike shi.”

More from this stream

Recomended