Majalisar dokokin Zamfara ta tsige kakakinta saboda tsanantar rashin tsaro a jihar

Majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige kakakinta, Bilyaminu Moriki, tare da nada Bashar Gummi, a matsayin kakakin majalisar.

Hakan ya biyo bayan kudirin da dan majalisa mai wakiltar mazabar Maru, Nasiru Abdullahi ya gabatar, inda mambobi 18 cikin 24 suka amince da shi.

Mambobin majalisar 18 daga cikin 24 sun amince da tsige kakakin yayin wani taron gaggawa da suka gudanar a daren Alhamis.

A cewar ‘yan majalisar, an dakatar da shugaban majalisar ne saboda kalubalen tsaro da ya addabi jihar ba tare da wani yunkuri da majalisar ta yi na dakatar da wannan barnar ba.

Mambobin sun bukaci shugaban majalisar da aka nada da ya yi amfani da mukaminsa wajen kawo karshen ‘yan fashi da suka kai ruwa rana. 

Daya daga cikin ‘yan majalisar, Shamsudeen Basko, mai wakiltar mazabar Talata Mafara, ya shaida wa mai goyon bayan shugaban majalisar cewa, batun rashin tsaro na daya daga cikin muhimman batutuwan da ya kamata a baiwa fifiko wanda ya kai ga dakatar da tsohon kakakin.

More from this stream

Recomended