Ƴan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutane 16 A Jihar Taraba

Mutane 16 ciki har da wani Rabaran  a ka sace a lokacin da wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kai hari kan wasu ƙauyuka uku dake ƙaramar hukumar Zing ta jihar Taraba ranar Juma’a da daddare.

A cewar wasu majiyoyi dake yankin ƴan bindigar su da yawa  sun kai hari ƙauyukan Dekko, Lama da Monkin ranar Juma’a da daddare inda suka yi garkuwa da mutane 16.

Mutanen ƙauyukan da dama sun samu raunin harbin bindiga lokacin da suke ƙoƙarin hawa saman tsaunuka a ƙoƙarin tserewa  a lokacin harin ƴan bindigar.

Ƴan bindigar dake kan babura an ƙiyasta cewa yawansu ya kai 100.

Wata majiya dake yankin ta bayyana cewa ƴan bindigar wani ɓangare ne na ƴan fashin daji da sojoji da mafarauta suka kora daga wasu tsaunuka dake ƙaramar hukumar Yorro ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar SP Usman Abdullah ya tabbatar da kai harin.

More from this stream

Recomended