Wasu da ba a san ko suwaye ba sun kashe, Sylvanus Namang mai magana da yawun jam’iyar APC ta jihar Filato a garin Pankshin dake ƙaramar hukumar Pankshin ta jihar Filato.
Wani jigo a jam’iyar ta APC da ya nemi a ɓoye sunansa ya faɗawa jaridar Daily Trust cewa marigayin ya mutu ne sanadiyyar raunukan da ya samu a harin da aka kai masa.
Ya bayyana marigayi Namang a matsayin aboki abun dogaro wanda ya mayar da hankali matuƙa wajen cigaban jam’iyar APC a dukkanin matakai inda ya ƙara da cewa jam’iyar za ta fitar da sanarwa nan gaba kaɗan kan mutuwarsa.
Jaridar Daily Trust ta gano cewa an kashe marigayin ne a wajen ɗakinsa na otal da misalin ƙarfe 07:30 na safe bayan da wasu ƴan bindiga suka buɗe masa wuta.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa marigayin ya bar gida ranar Asabar domin halartar bikin jana’iza a garin na Pankshin.