Tsohon Gwamnan Kaduna Ramalan Yero  Ya Koma Jam’iyar APC

Watanni biyar bayan ficewarsa daga jam’iyarsa ta PDP, Muktar Ramalan Yero tsohon gwamnan jihar Kaduna ya koma jam’iyar APC mai mulki.

Tsohon gwamnan da ya mulki jihar Kaduna tsakanin shekarar 2012-2015 ya sha kaye a hannun tsohon gwamna Mallam Nasiru El-Rufai a zaɓen shekarar 2015.

Da yake bayanin kan sauya shekar tasa Yaro ya ce tun bayan ficewarsu daga jam’iyar PDP jam’iyoyi da yawa sun tuntube shi ciki har da jam’iyar APC inda suka zauna suka tattauna.

Ya ƙara da cewa sakamakon tattaunawar ce tasa daga yau ranar 12 ga watan Faburairu shi da abokan tafiyarsa a siyasa sun koma jam’iyyar APC.

Tsohon gwamnan ya shawarci magoya bayansa da su shigo jam’iyar ta APC domin ba da ta su gudunmawar wajen gina ƙasa da kuma jihar Kaduna.

More from this stream

Recomended