Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya sun kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne da ake kyautata zaton yana da hannu wajen yin garkuwa da Nabeeha, diyar wani lauya a Bwari.
Idan ba a manta ba ‘yan bindiga sun sace kimanin mutane 19 daga rukunin gidaje na Sagwari da ke unguwar Dutsen-Alhaji a karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya.
Masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su N700m don sakin mutanen da suka kama.
Masu garkuwa da mutanen sun kashe hudu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, ciki har da Nabeeha Al-Kadriyar, daliba mai karatun digiri kuma ƴar aji 4 a fannin nazarin halittu a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da Folashade Ariyo ‘yar shekara 13.
An yi garkuwa da Nabeeha ne tare da wasu ’yan’uwanta shida.