An rantsar da Usman Ododo a matsayin gwamnan jihar Kogi.
Ododo ya karbi rantsuwar kama aiki a wurin bikin rantsuwa da aka yi a Lokoja babban birnin jihar.
Ododo wanda yayi takara a jam’iyar APC shi ne ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a cikin watan Nuwamba na shekarar 2023.
A zaɓen da aka gudanar Ododo ya samu kuri’a 446,237 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Murtala Ajaka na jam’iyar SDP wanda ya samu kuri’a 259,052.
Dino Melaye ɗantakarar jam’iyar PDP shi ne yazo na uku da kuri’a 46,362.
Manyan baƙin da suka halarci bikin rantsuwar sun haɗa da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, Abdullah Ganduje shugaban jam’iyar APC gwamna mai barin gado Yahaya Bello da sauran jiga-jigan gwamnati.