Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba sani ya bayar da umarnin bincike kan harin jirgin sama da ya kashe mutane da dama a ƙauyen Tudun Birni dake ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
A wata sanarwa ranar Litinin ya ce gwamnati ta kudirin aniyar ganin cewa hari makamancin wannan bai sake faruwa ba ana gaba.
Rahotanni sun bayyana cewa an jefa bam ne kan mutanen ƙauyen lokacin da suke gudanar da taron Maulidi.
Tun da farko rundunar sojan Najeriya ta amsa alhakin kai harin inda ta ce an kai shi ne a bisa kuskure.
Gwamnan ya ce tuni ya tura jami’an gwamnati ya zuwa ƙauyen domin zaƙulowa tare da ceto waɗanda abun ya shafa.
“Na kuma bayar da umarnin ɗauke waɗanda suka jikkata ya zuwa Asibitin Koyarwa na Barau Dikko domin samun kulawar gaggawa. Gwamnati ta dauki nauyin kuɗin maganinsu dana ɗawainiyarsu.” a cewar sanarwar.