Majalisar dokokin jihar Taraba ta amince gwamna Kefas ya ciwo bashin biliyan 206

Majalisar dokokin jihar Taraba ta amincewa gwamnan jihar, Agbu Kefas ya ciwo bashin biliyan 206 da miliyan 778.

An amince masa ya ciwo bashin ne domin aiwatar da wani kwarya-kwaryar kasafin kudi.

Majalisar ta amince da bukatar ne a yayin zamanta na ranar Juma’a.

Bashin za a ciwo shi ne daga bankunan kasuwanci na Zenith, United Bank for Africa, Fidelity da kuma Keystone domin aiwatar da ayyuka daban-daban a jihar.

Joe Bonzena kakakin majalisar dokokin jihar ya ce an zartar da kasafin kudin tare da amincewa a ciwo bashin domin gwamnan ya samu damar bijiro da ayyukan da za su saka walwala a zukatan al’ummar jihar da suka dade suna jira.

More from this stream

Recomended