Ganduje bai damu da binciken bidiyon dala ba—Tsohon Kwamishina

Muhammad Garuba, tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Kano a karkashin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ya ce tsohon gwamnan bai damu da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na sake bude binciken faifan bidiyon dala da ke nuna yana karbar cin hanci ba.

Shugaban hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Barista Muhuyi Magajin Rimin-Gado, ya yi alkawarin sake bude binciken da ake yi wa tsohon gwamnan.

Rimin-Gado ya ce “Kowane gwamna, mataimakin gwamna ko shugaban kasa mai ci yana da kariya, yanzu wannan kariya ta kare, hukumar za ta yi abin da ya kamata.”

Sai dai tsohon kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba, wanda abokin tsohon gwamnan ne, ya bayyana rashin damuwarsu game da lamarin a wata hira da BBC Hausa.

Related Articles