An ƙona a-daidaita-sahun da ake zargin an yi amfani da shi wajen ƙwacen waya

Wasu fusatattun matasa da ke Kofar Kabuga da ke a Jihar Kano sun ƙone wani a-daidaita-sahun da ake zargin cewa an yi amfani da shi wajen ƙwacen waya.

Rahotannin da muka samu sun nuna cewa waɗanda suke cikin a-daidaita-sahun sun samu sun tsere.

Wannan lamari dai ya faru ne a daren jiya Asabar.

Matsalar ƙwacen waya da kashe mutane dai ya yi ƙamari a Arewacin Najeriya musamman Kano, inda kusan kullum sai an samu rahotannin aikata wannan mummunan aiki.

More from this stream

Recomended