Gwamnatin tarayya ta gurfanar da wasu yan kasar China uku a gaban wata babbar kotun tarayya dake birnin Abuja inda ake zargin su da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
Hukumar tsaron Civil Defense ce ta gurfanar da mutanen a gaban kotun a madadin gwamnatin tarayya.
Mutanen da ake zargi da kuma kamfanin su Lian Hua Quarry Nigeria Limited ana musu tuhume-tuhume uku da suka haɗa da haɗa baki da kuma haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.
Lauya mai gabatar da aka ƙara, Alex Ojo ya bukaci a tsare waɗanda ake zargi a gidan yari har zuwa lokacin da za a fara sauraron shari’ar.
