Atiku ya kai ziyara Amurka

Mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kai ziyara kasar Amurka.

A cikin wasu hotuna da ya wallafa a shafukansa na soshiyal midiya Atiku ya sanar da cewa ya sauka a birnin Washington.

Ya kai ziyarar ne bisa amsa gayyatar da cibiyar kasuwancin Amurka ta yi masa.

A yayin ziyarar Atiku na tare da wasu jiga-jigan jam’iyar PDP.

More from this stream

Recomended