Akwai wani babur ɗin roba na wasa da aka ajiye a kusurwar gidan Mariam Kuyateh. Babur ɗin duk ya yi ƙura.
Asali babur ɗin na ɗanta ne mai watanni 20 da haihuwa mai suna Musa wanda ya rasu a watan Satumba.
Yana daga cikin yara 66 da suka rasu a Gambia sakamakon wani maganin tari da ake kyautata zaton sun sha wanda ya jawo musu ciwon ƙoda, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana.
Babu wani a gidan da ke taɓa babur ɗin wasan na Musa – wanda wani abu ne da ke tuna abin da aka rasa.
Mahaifiyarsa mai shekara 30, wadda ke da ƴaƴa huɗu, tana ta hawaye a yayin da take tuna abin da ya faru da ɗanta.
A yayin da take zaune a gidanta a wajen birni mafi girma na Gambia wato Serrekunda, ta yi bayani dalla-dalla kan yadda ciwonsa ya fara a matsayin mura.
Bayan likita ya duba sa, sai mahaifinsa ya siyo masa maganin tari domin shawo kan matsalar.
“Ko da aka ba shi maganin, sai murar ta tsaya, amma kuma ta jawo wata matsala,” in ji Ms Kuyateh.
“Ɗana ba ya iya fitsari.” in ji ta.
Sai ta koma asibiti inda aka yi wa Musa gwajin jini wanda gwajin ya nuna cewa yana ɗauke da zazzaɓin Maleriya.
Sai aka sake ba shi wani maganin har aka saka masa katata amma duk da haka ya kasa yin fitsarin.
A ƙarshe dai sai dai aka yi wa ƙaramin yaron tiyata. Babu wani ci gaban da aka samu. “Ya kasa warkewa, sai ya rasu.”
Asalin hoton, KUYATEH FAMILY
A farkon makon nan ne dai Hukumar Lafiya Ta Duniya ta fitar da wani gargaɗi kan wasu magunguna huɗu da ke da alaƙa da mace-mace a Gambia.
Magungunan sun haɗa da Promethazine Oral Solution da Kofexmalin Baby Cough Syrup da Makoff Baby Cough Syrup da Magrip N Cold Syrup waɗanda wani kamfanin Indiya ne yake haɗa su mai suna Maiden Pharmaceuticals.
Kamfanin dai ya gaza wurin tabbatar da ingancinsu, kamar yadda WHO ta bayyana.
Gwamnatin India dai ta soma bincike kan wannan lamari. Sai dai kamfanin bai ce komai ba ko da BBC ta so jin ta bakinsa. Jama’a da dama dai sun fusata kan lamarin da ya faru a Gambia.
Akwai mutane da dama da suke t akira ga ministan lafiya na ƙasar Dakta Ahmadou Lamin Samateh, tare da kama waɗanda suka shiga da magungunan a cikin ƙasar.
“Rai 66 na da yawa. A don haka muna buƙatar adalci, saboda waɗanda lamarin ya faru da su yara ne da ba su yi komai ba,” in ji Ms Kuyateh.
Asalin hoton, OMAR WALLY
Haka kuma akwai Aisha ƴar wata biyar wadda ita ma ta rasu sakamakon waɗannan magunguna.
Mahaifiyarta, Mariam Sisawo wata safiya ta gano cewa bayan ƴarta ta sha maganin tarin, sai ta kasa yin fitsari.
Bayan ta je asibiti, sai aka shaida wa Mariam mai shekara 28 da cewa babu wani abu da ke damun ƴarta.
Sai da mahaifiyar Aisha ta yi sawu biyu zuwa asibiti kafin aka mayar da ita zuwa wani asibiti da ke Banjul babban birnin ƙasar wanda ke da nisan kilomita 36 daga gidansu da ke Brikama, amma bayan an shafe kwana biyar ana ƙoƙarin yi mata magani, sai ta rasu.