‘Yan bindiga sun sace wani basarake a jihar Plateau.
Basaraken Da Gyang Balak, yakasance mai fada aji a gundumar Vwang da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.
Dan Majalisar dake wakiltar karamar hukumar a majalisar dokokin jihar ne ya tabbatarwa da jaridar Punch labarin sace basaraken.
An sace basaraken ne a ranar Lahadin data wuce da misalin karfe 8 na dare.
Rahotanni sun ce an sace shi ne a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta komawa gida a kan titin dake yankin Kuru.
Lamarin ya faru ne kasa da wata guda bayan da wasu ‘yan bindigar suka sace wani basarake a karamar hukumar Mangu wanda daga bisani suka sake shi bayan biyan kudin fansa.